Ziyara shugaban hukumar agajin abinci ta majalisar Dinkin Dunia a Niger da Mali | Labarai | DW | 28.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaban hukumar agajin abinci ta majalisar Dinkin Dunia a Niger da Mali

Shugaban hukumar bada agajin abinci ta Majalisar Dinkin Dunia wato PAM, ya kammala ziyara aiki ta yini 2 ,da ya kai a kasar Mali.

A lokacin wannan ziyara da ya fara tun ranar assabar, James Morris ya gana da hukumomin kasar, inda su ka tantana batutuwan matsalolin yinwa, da Mali ta yi fama da su ,a watanin baya.

Yayi yabo, da jinjinna damtse, ga gwamnati a game da matakkan da ta dauka, na mangace matsalar karancin abinci.

A daya hannun, sun yi masanyar ra´ayoyi a kan halin da a ke ciki a damanar shekara banna.

A jimilce kasar Mali ta kubuta a banna da bila´in yinww, to saidai hukumomin kasar sun kara tara kokon bara, kamar da abin nan da bahaushe ke cewa, ko da mutum na da kayu, to ya kara da wanka.

Bayan kasar Mali shugaban hukumar PAM zai ziyarci jamhuriya Niger.

A halin da ake ciki a wannan kasa, wata sabuwar cecekuce ta kunno kai, a game da matsalar abinci.

A makon da ya gabata hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Dunia, ta buga labarin cewa, a shekara banna ma a kalla mutane million 3, za su fuskanci matsalar yinwa.

Gwamnatin Jamhuriya Niger, ba da wata wata ba ta karyata wannan zance da a cewar ta ba shi da tushe, bare makama.