Tsagerun Niger Delta mutane da suka dauki makamai don yin rikici da hukumomi a kudu maso kudancin Najeriya inda ake tono man fetur.
Sau tari wadannan tsageru sun sha tada bam da kuma sace ma'aikatan mai don matsawa gwamnati lamba kan ta biya musu wasu bukatunsu. Gwamnatin Najeriya dai na daukarsu a matsayin 'yan ta'adda.