Asari Dokubo daya ne daga cikin masu fafutuka ta kwato 'yancin Niger Delta mai arzikin man fetur a Najeriya.
Shi da 'ya'yan kungiyarsa sun sha daukar makamai don yin fito na fito da hukumomin Najeriya kan yankin nasu. Lokacin da Goodluck Jonathan ke mulki, Asari da abokan burminsa sun dakatar da tada kayar bayan da suke yi.