Yan siyasa na neman tsauraran matakan tsaro a Jamus | Labarai | DW | 06.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan siyasa na neman tsauraran matakan tsaro a Jamus

Yan siyasa dake nan tarayyar jamus sunyi kira da a kara daukar matakai tsaurara na yaki da ayyukan tarzoma da dokokin shigowa cikin kasar,bayan cafke wasu mutane uku da ake zargi da shirin kai hari da yansanda sukayi a kasar.Jammiyyar yan mazan jiya dake jagorancin kasar ,ta bukaci da adauki tsararan matakai na hukunta wadanda hukumin sukace na ziyaratan sansanonin horarwa na yan tarzoma,ta hanyar binciken wadannan mutane ta yanar gizo gizo.A yanzu haka dai jamian yansan dake nan jamus sun kaddamar da bincike na hadin gwiwa da kasashen ketare akn wasu mutane 10,da akace suna da hannu a harin da mutane ukun da aka cafke suka shirya kaiwa,a filin saukar jiragen sama da sansanbin dakarun Amurka dake nan Jamus.A ranar talata nedai jamian tsaro suka cafke wasu jamusawa guda biyu da suka musulunta da wani baturke guda,akan zargin su da kasancewa yan tarzoma.