Sin ta saka wa wasu kasashen EU takunkumi | Labarai | DW | 23.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sin ta saka wa wasu kasashen EU takunkumi

Faransa da Jamus da wasu da ke cikin kungiyar EU sun kira jakadun Chaina da ke kasashensu domin nuna kin amincewarsu da takunkumin da Chaina ta dora a kan wasu 'yan kasarsu.

Wannan takadamar na zuwa ne bayan da a jiya Litinin kasashen EU da Birtaniya gami da kasar Kanada suka kakaba wa wasu tsaffin jiga-jigan gwamnati na da da na yanzu takunkumi. Amirka wacce ita ce ta fara maka wa jami'an na Chaina takunkumi yanzu haka ta kara ma wasu mutum biyu.


Wadannan takunkumai ga Chainar na da nasaba da zargin tauye hakkin bil'Adama da suke ke yi a kan tsirarun Musulmai 'yan kabilar Uyghur, wanda Chainar ta sha musantawa a lokuta da dama.

Yanzu dai sama da kasashe 10 da ke Kungiyar Tarayar Turai ne Chaina ta saka wa takunkumin hana su shiga kasar a wani abu da ke zama na ramuwar gayya.