Shugaba China Hu Jintao ya fara ziyarar aiki a Jamus | Labarai | DW | 11.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba China Hu Jintao ya fara ziyarar aiki a Jamus

Shugaban China Hu Jintao ya fara wata ziyarar kwanaki 4 a nan Jamus. A lokacin da yake tarbarsa shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler yayi kira da a shimfida sahihiyar demukiradiya a China. Köhler ya ce tattalin arziki ya fi bunkasa ne a wuraren da ake da jama´a ke da cikakken ´yancin walwala. Köhler ya ce a ko-ina cikin duniya mutane na son a ba su ´yancin walwala tare da girmama hakokin su. A lokaci daya kuma Köhler ya yabawa canje-canjen da hukumomin China ke aiwatarwa musamman wajen bude kofofin kasar ga kasashen waje. Shugabannin biyu sun shaida wani bikin sanya hannu kan jerin kwagila tsakanin manyan ´yan kasuwar China da Jamus ciki har da har da ta sayen jiragen kasa masu gudun gaske har guda 60 da kudin su ya kama Euro miliyan 670 daga Jmaus. A yau shugaba Hu zai gana da shugaban gwmnati mai barin gado Gerhard Schröder da shugabar jam´iyar CDU Angela Merkel.