Sharhi: Nasara ga demokaradiyyar Najeriya | Siyasa | DW | 01.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Nasara ga demokaradiyyar Najeriya

A karon farko 'yan Najeriya sun yi amfani da kuri'unsu wajen kawar da wata gwamantin farar hula. Wannan dai babban ci gaba ne ga demokaradiyya a kasar, inji Thomas Mösch shugaban sashen Hausa na DW a cikin wannan sharhi.

Thomas Mösch ya fara sharhin ne da cewa: Kalmar da ya kamata a furta game da zaben Najeriya ita ce "barka da arziki". Ba wai don madugun 'yan adawa Janar Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa ba, amma kuma sai don cewa wannan shi ne karon farko da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata zababbiyar gwamnati tun bayan da tarayyar Najeriya ta koma kan tafarkin demokaraydiyya. Wannan ya na nuna irin yadda wannan tsari na demokaradiyya ya fara tsayawa a kan kafafunsa a wannan kasa.

Dalilai da dama ne dai suka sa aka samu wannan ci gaba a Najeriyar. Da farko dai jam'iyyun adawa da dama sun hada karfi da karfe karkashin gamayya ta APC, don ganin cewa hakarsu ta cimma ruwa a wannan karon. Sannan kuma sun yi amfani da sahihiyar hanya wajen fidda janar Muhammadu Buhari a matsayin gwaninsu a zaben shugaban kasa na 2015. Da ma dai yana da gagarumar goyon baya a arewacin kasar da ke zama yankinsa na asali. Amma kuma a wannan karo ya samu hadin kan Yarbawa a yakin kudu maso yammacin kasar musamman ma a Legas da ke zama cibiyar cinikayyar tarayyar ta Najeriya.

Jonathan ya yi ragwan azanci

Amma kuma yabo ya tabbata ga shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan dangane da hanzarta bayyana shan kaye da ya yi tare da taya Buhari murnar lashe zaben, tun ma kafin INEC ta sanar da sakamakon zabe na din-din-din. Mataki ne da ba a saba gani ba, ba ma a Najeriya kadai ba, har da kasashen Afirka da dama.

Deutsche Welle Afrika Haussa Thomas Mösch

Shugaban sashen Hausa na DW, Thomas Mösch

Amma dai a hakikanin gaskiya Jonathan shi ya sayi ruwan dafa kansa, domin bai taba nuna wa 'yan arewa ya san da su ba, ballantana ma ya magance matslar tsaro da ta addabesu ba. Sai da zabe ya karato ne ya farka a makare daga barci, lamarin da ya sa daidai da Kiristocin arewacin Najeriya suka juya masa baya.

Jega ya taka rawar gani

Sai dai kuma za a yi tuya a manta da albasa idan ba a sanya rawar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Attahiru Jega ya taka ba. Wannan shehun malamin kimiyyar siyasa ya shafe makwanni yana fama da matsin lamba. Na farko daga gwamnati wacce ta yi amfani da dalilai na tsaro wajen tailasta masa dage zabe da makawanni shida. Sannan kuma 'yan kanzagin Goodluck Jonathan sun ta nema a tsigeshi daga mukaminsa, saboda sun ta nema ya yi watsi da tsarin amfani da na'u'rori wajen gudanar da zabe, amma kuma ya dage a kan bakarsa. A takaice dai Jega ya bai wa marada kunya, saboda ya gudanar da zaben cikin tsafta kuma ba tare da tashin hankali na azo a gani ba. Babu dai wata tawaga ta 'yan sa ido a zabe ko da daya da ta sokeshi da yin ba daidai ba.

Kalubalen da ke gaban Buhari

A yanzu dai mayar da Najeriya kan kyakkyawar turba ta zama babban kalubale ga Muhammadu Buhari. Kudin da gwamnati ke shigarwa aljihunta ya ragu sakamakon faduwar farashin man fetur, wanda kasar ke dagora a kai wajen samun masu gida rana. Ga shi kuma har yanzu da sauran rina a kaba dangane da yaki da kungiyar Boko Haram. Kasancewar ma shi Buhari dan asalin arewacin Najeriya ne, ya kamata ya fi Jonathan gano bakin zaren murkushe wadannan tsageru. Sai dai kuma ya kwana da sanin cewa ba wai mataki na soji domin murkushe 'yan Boko Haram yakin arewa maso gabashin Najeriya kawai ke bukata ba, amma kuma har da gudanar da ayyukan da za su ciyar da wannan yanki gaba.

Wani babban kalubale da Buharin zai fuskanta bayan saukan Jonathan daga mulki shi ne na tayar da kayar baya daga tsagerun yankin Niger Delta. Gwamnatin Jonathan ta kyalle 'yan bindigan wannan yanki mai arzikin man fetur sun ci karansu ba tare da babbaka ba. Saboda haka za su so Buhari ya ci gaba da sakar musu mara. Buhari har wa yau yana da jan aiki a gabansa wajen sa kafar wando guda da rub da ciki da dukiyar kasa da ya zama ruwan dare tsakanin manyan jami'an gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin