Goodluck Jonathan tsohon shugaban Najeriya ya mulki kasar daga shekara ta 2010 zuwa 2015, ya dauki madafun iko bayan mutuwar marigayi Umaru Musa Yar'Adua.
Jonathan ya fara da mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa da ke yankin kudu masu kudancin kasar lokacin da Najeriya ta koma tafarkin demokaradiyya a 1999, sannan daga nan ya zama gwamnan jihar, kana a zaben shekara ta 2007 ya zama mataimakin shugaban kasa, kafin ya zama shugaban kasa a shekara ta 2010. Amma ya fadi a zaben shekara ta 2015.