Sa wa makaranta sunan Merkel a Nijar | Zamantakewa | DW | 17.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sa wa makaranta sunan Merkel a Nijar

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sauya sunan makarantar Goudel da ke birnin Yamai zuwa sunan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Gwamnatin Nijar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da matakin hukumomin gudanarwa ta makarantar Firamare na unguwar Goudel da ke birnin Yamai fadar gwamnatin kasar, sakamakon hulda ta fahimmata da ke tsakanin kasar Jamus da Jamhuriyar Nijar.

Matakin maye sunan makarantar zuwa sunan Merkel, baya rasa nasaba da jin dadi daga wata ziyarar da taba kaiwa makarantar a lokutan baya, inda ta ba da gagarumar gudumuwar inganta dakunan karatun dalibai da ke cikin makarantar.

Jami'an ofishin jakadancin Jamus da ke Jamhuriyar Nijar, sun bayyana jin dadi kan wannan mataki da hukumomin makarantar suka dauka na sadaukar da sunan makarantar ga shugabar gwamnatin ta Jamus, sun kuma ce matakin zai kara kulla dangon zumunci tsakanin kasashen biyu ta yadda zai ba da damar inganta harkar Ilimi a Nijar.