Rasha ta sanarda korar wasu jami′an diplomasiya na Burtaniya | Labarai | DW | 19.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta sanarda korar wasu jami'an diplomasiya na Burtaniya

Kasar Rasha ta sanarda korar wasu jamian diplomasiya na Burtaniya su 4 daga kasarta,ta ce zata janye hadin kai da take baiwa Burtaniya game da yaki da taadanci,ta kuma rage takardun visa ga jamian kasar

Rahotanni daga birnin Moscow sunce gwamnati ta kirawo jakadan Burtaniya a Rasha Tony Brenton saoi kadan kafin wani taron manema labarai game da danganta tsakanin kasashen biyu.

Jakadan ya baiyana cewa gwamnatin Rashan ta bashi wasu sakonni ga gwamnatin Burtaniya inda aka baiyana korar jamian na Burtaniya.

Dama tuni kasar Burtaniyan take dakon martanin Rasha game da korar wasu jamianta na diplomasiya 2 daga London game da batun kisan tsohon jamiin leken asirin Rasha.

A wani labarin kuma kasar rasha ta baiyana cewa suka da Kungiyar Taraiyar Turai tayi game da rikicin diplomasiya tsakanin Rasha da Burtaniya cewa zai shafi danganta tsakanin Rashan da kungiyar.