David Cameron na daya daga cikin manyan 'yan siyasar Burtaniya kuma memba ne na jam'iyyar Conservative.
Cameron ya zamanto firaministan Burtaniya a shekara ta 2010 lokacin da ya yi hadaka da jam'iyyar Liberal Democrats sai dai a shekara ta 2015 jam'iyyarsa ta samu gagarumin rinjaye a zaben da aka yi wanda ya sanya ta kauracewa yin kawance da wata jam'iyyar.