1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarauniya Elizabeth ta cika shekaru 96

Abdourahamane Hassane MNA
April 21, 2022

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, wacce ita ce sarauniya mafi tsufa a duniya, ta cika shekara 96 ​da haihuwa.

https://p.dw.com/p/4AB0c
Großbritannien | Queen Elizabeth | Thronjubiläum
Hoto: Joe Giddens/PA Wire/dpa/picture alliance

Saurauniyar wacce ta janye daga harkokin gudanar da masarautar saboda matsalar kafafu da tsufa wadda ke yin amfani da keken guragu wajen yin kai da kawonta, a wannan rana ta Alhamis ta cika shekaru 96. Tun a cikin watan Oktoba, ta wakilta danta yarima Charles, mai shekaru 73, wanda zai gajeta domin tafiyar da harkokin mulki.

An dai shirya yi mata biki na musammun, inda za a yi harbin igwa daga hasumiyar fadar Hyde Park da ke a birnin London domin nuna murnar zagayowar ranar haihuwarta.