Rangadin tawagar EU a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rangadin tawagar EU a gabas ta tsakiya

A cigaba da rangadin da ta kai a yankin gabas ta tsakiya, komishinar hulɗa da ƙetare, ta ƙungiyar gamaya turai, Benita Ferrero Waldner, ta alkwarata wa Palestinawa cewar, ko wuya ko daɗi EU, ba zata watsi da wasu ba.

Komishinar ta ce, idan so samu ne, Palestinawa su amince da shawarwarin ƙasashe masu shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya,wato ɗaukar Isra´ila a matsayin halataciyar ƙasa, da kuma daina kai hare-hare, ga bani yahudu, to amma idan ma hakan ba ta samu ba, EU a shirye ta ke, ta ci gaba da agazawa Palestinawa, ta la´akari da matsanancin halin da su ke ciki.

A yayin da ta gana da hukumomin Jordan, ta bayyana tallafin Euro milion 265, domin taimakawa wannan ƙasa, ta gudanar da cenje-cenje, ta huskar tattalin arziki, dokoki, da kuma kyautata rayuwar jama´a.