Merkel ta bukaci samar da asusun bai daya | Labarai | DW | 19.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta bukaci samar da asusun bai daya

A ci gaba da lalubo bakin zaren takaddamar bakin haure a tsakanin mambobin kungiyar EU, shugabar gwamnatin Jamaus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bayyana bukatar samar da kudaden kasafi na bai daya.

Da yake tsokaci bayan ganawarsa da Merkel a garin Meseberg castle da ke kusa da birnin Berlin, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce tsare-tsaren yadda za a zuba kudade a asusun batu ne zai bukaci tattaunawa da sauran takwarorinsu.

Ganawar shugabannin biyu ya samar da matsaya kan rage radadin kwaraarr 'yan gudun hijira da kuma maidasu kasar da suka fara yin rejista nan take. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar CSU da ke kawancen mulki ke matsa wa Merkel lamba kan neman mafita ga matsalolin 'yan gudun hijira da sauran kasashen Turai.