1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin gwamnatin Jamus kan rikicin Ukraine

March 20, 2014

A jawabin da ta yi a Berlin shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana matsayin kasar game da rikicin Ukraine. Sai dai akwai batutuwa da yawa da taron EU a birnin Brussels zai duba.

https://p.dw.com/p/1BTO3
Angela Merkel Regierungserklärung 20.3.14
Hoto: Reuters

Tarayyar Jamus ba za ta nemi taron kolin yini biyu na shugabannin kasashen tarayyar Turai da aka fara a wannan Alhamis a birnin Brussels, ya sanya wa Rasha tsauraran takunkuman karya tattalin arziki ba. Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lokacin jawabinta ga majalisar dokoki ta Bundestag a birnin Berlin game da matsayin Jamus a kan rikicin Ukraine.

Ko da ya ke a jawabin ga majalisa dokokin ta Bundestag Merkel ta fito karara ta nuna matsayin kasarta game da rikicin na Ukraine, da cewa ba za ta nema da a tsaurara takunkuman tattalin arziki a kan Rasha ba, amma ta ce za a kara rufe ajiyar bankin wasu daidaikun mutane da hana su yin tafiye-tafiye a matsayin mataki na biyu na jan kunne wanda tun a ranar 6 ga watan nan na Maris kungiyar EU ta dauka. Amma kuma matukar halin da ake ciki a gabaci da kudancin Ukraine ya ta'azzara to EU za ta dauki mataki na uku wato takunkuman karya tattalin arziki a kan Rasha.

"A ranakun Alhamis da Juma'a majalisar zartaswar EU za ta nuna a fili cewa a shirye take na tsaurara takunkuman a duk lokacin da yin haka ya ta so, wato takunkumai na mataki na uku kuma ko shakka babu za su kasance takunkuman karya tattali arziki."

Karin matsin lamba kan Rasha

Ban Ki Moon bei Putin 20.03.2014
Ban Ki Moon da Vladimir Putin a RashaHoto: Reuters

Bugu da kari Merkel ta sanar da karin takunkumai don matsa kaimi a kan Rasha, tana mai cewa shugaba Vladimir Putin ya mayar da kanshi saniyar ware bisa amincewa da shigar da yankin Kirimiya cikin kasar abin da ya saba da dokokin kasa da kasa. Saboda haka ta saka ayar tambaya game da yiwuwar gudanar da taron kungiyar G7 hade da Rasha da tattaunawa tsakanin gwamnatocin Jamus da Rasha.

"Matukar babu wani fage na siyasa ga wata muhimmiyar kungiyar irin su G8, to ke nan babu kungiyar G8 kuma babu zancen wani taron koli mai irin wannan siga."

A lokaci daya Merkel ta sanar da ba da tallafi ga Ukraie mai fama da rikice-rikice. Ta ce ana samun ci gaba a tattaunawar da ake da Asusun IMF game da tallafi ga gwamnatin birnin Kiev. A matsayin wata alama ta nuna wa Ukraine zumunci a siyasance, Merkel ta yi nuni da sanya hannu da za a yi kan bangaren siyasa na yarjejeniyar shigar da ita cikin EU a ranar Jumma'a.

Korafi kan sanya takunkumi

Gregor Gysi Bundestag 13.03.2014
Gregor Gysi: Kasashen yamma sun tabka kuskureHoto: picture-alliance/dpa

Sai dai jam'iyyar adawa ta Linke ta yi suka, wanda shugaban bangarenta a majalisar dokoki, Gregor Gysi ya ba da shawara da a shiga tattaunawa da Rasha kana kuma dukkan bangorin biyu su amsa cewa sun tabka kurakurai. Gysi ya ce takunkumai ba za su kai ga samun maslaha ba.

"Shin ta yaya za a iya kawo karshen takunkuman? Shin idan Kirimiya ta koma karkashin Ukraine, idan ba ta koma ba fa? Za a ci gaba da sanya takunkumi ne? Tun yanzu na fara jin ana magana yadda ake son a cire takunkuman sannu a hankali bayan shekara daya ko biyu."

Merkel dai ta samu goyon baya ga alkiblar da ta dauka ga rikicin na Ukraine da ke zama wani bangare na jawabinta. Ta dai tabo batutuwa da dama ciki har da matakan magance rikicin kudi da samar da aikin yi da kuma karfafa huldar kasuwancin cikin gida a tsakanin kasashen EU.

Mawallafa: Kay-Alexander Scholz / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar