Vladimir Putin mutum ne da ya rike matsayi na firaminista da kuma shugaban Rasha a lokuta daban-daban. Ya na daya daga cikin mutanen da dake da karfin fada a ji a zamaninsa.
Baya ga mukamin na shugaban kasa da ya rike, Putin ya yi aiki da hukumar leken asirin Rasha ta KGB na tsawon lokaci kafin daga bisani ya shiga harkokin siyasa.