1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Jamus na son a sulhunta rikicin Ukraine da Rasha

Abdoulaye Mamane Amadou
October 16, 2024

A yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin Jamus, shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz, ya bayyana manufofin gwamnatinsa na sulhunta rikicin Rasha da makwabciyarta Ukraine.

https://p.dw.com/p/4lsxU
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz lokacin da yake jawabi a gaban majalisar dokoki ta Bundestag
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz lokacin da yake jawabi a gaban majalisar dokoki ta BundestagHoto: Juliane Sonntag/IMAGO

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kira da a dakatar da bata-kashin da ake a tsakanin Ukraine da Rasha ko da kuwa abin zai kai ga a tattauna ne da shugaba Vladimir Putin.

Da yake jawabi a gaban majalisar dokoki ta Bundestag, Olaf Scholz ya ce duk da sahihin goyon bayan da kasarsa da abokan dasawarta ke ba wa Ukraine, kamata ya yi su yi duk mai yiwuwa don kashe wutar rikicin.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya kuma kara da cewa "A shirye muke idan har an ba mu wannan damar mu tauna batun da Shugaba Putin", sai dai ya kara da cewa amma ba tare da daukar wani matakin da zai raunata Ukraine ko kuma kasa tuntubar abokan huldarta ba.