Labarin Wasanni: Sakamkon wasannin mako | Zamantakewa | DW | 27.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin Wasanni: Sakamkon wasannin mako

Ko kun san yadda sakamakon wasannin lig na Jamus na Bundesliga da wasu kasashen Turai a karshen mako ya kasance? Shirin Labarin Wasanni.

 1. Bundesliga | RB Leipzig vs Hertha BSC

RB Leipzig ta lallasa Hertha Berlin a filin wasa na Red Bull Arena

A sakamakon wasannin Bundesliga na Jamus, kungiyar Bayern Munich ta bi Greuther Fürth har gida ta lallasa ta da ci uku da daya, sannan Union Berlin ta doke Arminia Bielefeld da ci daya mai ban haushi, kana Hoffenheim ta doke Wolfsburg da ci uku da daya, yayin da Leverkusen ta samu galaba kan Mainz ita ma da ci daya mai ban haushi. Ita kuwa kungiyar Eintract Frankfurt ta tashi kunnen doki daya da daya da kungiyar FC Cologne, sannan Mönchengladbad ta doke Dortmund da ci daya mai ban haushi kana RB Leipzig ta yi cin kacar tsohon keke rakacau shida da nema kan kungiyar Hertha Berlin.

Fußball Premier League Manchester United - Aston Villa

Manchester United ta sha kashi a gida a hannun Aston Villa

A wasannin lig na Preimier na Ingila kuwa, kungiyar Manchester United ta sha kaye a gida a karon farko tun da aka fara kakar wasannin a wannan shekara, inda Aston Villa ta doke ta da ci daya mai ban hasuhi, kuma dan wasan Manchester United Bruno Fernandes ya zubar da damar da kungiyar ta samu na rama wannan kwallon, lokacin da ya watsar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a mintuna na karshe na wasan. Ita ma kungiyar Chelsea ta doke Manchester City da ci daya da nema, yayin da Brentford ta tashi canjaras uku da uku a wasa tsakaninta da Liverpool, sannan Leicester ta tashi biyu da biyu da kungiyar Burnley. A wasannin La Liga na kasar Spain kuwa, kungiyar Valencia ta tashi kunnen doki daya da daya da Athletic Bilbao, ita kuma Sevilla ta doke Espanyol ci biyu da nema, yayin da Real Madrid ta tashi canjaras babu ci a wasa tsakaninta da Villarreal, ana ta bangaren kungiyar Barcelona ta doke Levante da ci uku da nema.

Sauti da bidiyo akan labarin