Kungiyar AU ta zargi Sudan da kai sabbin hare hare a Dafur | Labarai | DW | 19.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar AU ta zargi Sudan da kai sabbin hare hare a Dafur

Kungiyar gamaiyar Afrika ta zargi gwamnatin Sudan da kungiyar yan tawayen Janjaweed da kai wasu sabbin hare hare a Dafur. Kungiyar ta gamaiyar Afrika wadda ke da dakarun kiyaye zaman lafiya 7,000 a yankin mai fama da rikici tace farmakin da aka kai ta sama da kuma ta kasa ya hallaka fararen hula tare kuma da jikata wasu da dama. Jamian kungiyar ta hadin kan Afrika sun baiyana harin da cewa ya sabawa yarjejeniyar tsaro ta kare lafiyar jamaár Dafur. Da yake maida martani bayan aukuwar hare haren shugaban hukumar taimakon jin kai na Majalisar dinkin duniya Jan Egeland ya bukaci gwamnatin ta Sudan ta hada kai da majalisar dinkin duniya domin kawo karshen wahalhalun da jamaá suke fuskanta. Har ya zuwa wannan lokacin dai babu wani martani daga gwamntain a birnin Khartoum.