Jamus ta fadada matakan tsaro | Labarai | DW | 03.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta fadada matakan tsaro

Ministan harkokin cikin gida na Jamus Wolfgang Schäuble,ya bayyana manufofin kasarsa adangane da matakan tsaro cikin watanni shida da zata jagoranci kungiyar EU.Scäuble ya fadawa taron manema labaru a birnin Berlin cewa ,jamus zata bukaci fadada auyukan yansandan kasa da kasa na turai ,da hukunar yansanda na kasashen turai ,a kokarinta na yaki da ayyukan tarzoman kasa da kasa da kuma sauran miyagun ayyuka na kann iyakokin kasashe.Haka zalika ministan cikin gidan jamus din,yace ayayi da take kann wannan mukami,kasarsa zata mayar da hankali kann harkokin shige da ficen kasashen.