1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce Hamas ce ke rura wutar rikicin ta da Isra'ila

November 16, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga 'yan kungiyar Hamas da su gaggauta dakatar da harba rokoki cikin Isra'ila don kawo ƙarshen rikicin yankin.

https://p.dw.com/p/16kS5
Israel Angriffe auf GazaHoto: Reuters

A wani jawabi da ya yi ga manema labarai, mai magana da yawun shugaba Merkel wato Georg Streiter ya ce shugabar gwamnatin ta Jamus ta damu matuƙa game da halin da ake ciki inda ya ce Merkel din Hamas ce kanwa uwar gami a rikicin na baya-bayan nan kuma Isra'ila na da dukannin 'yanci na kare al'ummarta.

To yayin da shugabar gwamnatin ta Jamus ke wadannan kalamai, a hannu guda kuma shugaba Muhammad Mursi na Masar Allah wadai ya yi da harin da ya ce Isra'ila na kaiwa zirin na gaza inda ya ce wannan mataki ne tauye hakkin bani adama.

Kamfanin dillacin labaran na Masar MENA ya rawaito shugaba Mursi bayan kamamla sallar Juma'a ya na cewa Masar ba za ta zuba idanu ta na ganin Gaza na fama da wannan matsala ba inda ya ƙara da cewar Masar ɗin yanzu ba irin ta da ba ce kuma larabawa da ake da su yanzu sun sha ban-ban da wanda ake da su a baya.

Ita kuwa ƙasar Tunisia a nata ɓangare cewa ta yi za ta tura ministan harkokin wajenta Rafik Abdesslem zuwa zirin na Gaza a gobe Asabar idan Allah ya kaimu domin bada ƙwarin gwiwa ga 'yan Hamas ɗin a rikicin da su ke yi da ƙasar ta bani yahudu kamar dai yadda kakakin shugaban ƙasar ta Tunisia Moncef Marzouki ya shaidawa manema labari.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman