Jamus ta bayar da umarnin jigilar fasinjoji zuwa ƙasar. | Labarai | DW | 20.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bayar da umarnin jigilar fasinjoji zuwa ƙasar.

Hukumomin Jamus sun umarci Lufthansa da Air Berlin su yi jigilar fasinjoji 15,000 zuwa ƙasar

default

Ministan kula da harkokin sufuri a Jamus Peter Ramsauer ya sanar da cewar za'a sami daidaiton lamura a sha'anin zurga - zurgar jiragen sama a yau Talata ko da shike kuma ya ce hakan zai kasance ne a ƙarƙashin tsaurarar matakan tsaro. Hukumar kula da sufurin jiragen sama a nan Jamus ta baiwa kamfanonin jiragen sama na Lufthansa da kuma Air Berlin umarni na musamman domin ɗauko fasinjoji dubu 15 zuwa Jamus waɗanda ke filayen jirage daban daban a wasu ƙasashe amma jiragen zasu yiwo ƙasa ne daga gajimaren tokar kana a ƙarƙashin kulawa ta musamman.

Matakin da Jamus ɗin ta ɗauka dai ya biyo bayan yarjejeniyar da ministocin kula da harkokin sufuri na ƙungiyar tarayyar Turai suka cimma ne ta sassauta matsayin yankunan da aka taƙaita zurga - zurgar jiragen sama sakamakon gajimaren toka daga aman wuta na wani tsauni dake ƙasar Iceland.

A halin da ake ciki kuma jami'an kula da harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar Birtaniya sun sanar da cewar, alamu na nuna tokar aman dutse daga ƙasar Iceland ɗin yana ƙara yin muni, lamarin dake janyo rashin tabbas na ko za'a yi dawo da jigilar jiragen sama a filin jirgin samar birnin London.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu