Jamus ta bada karin tallafi wa Somalia | Labarai | DW | 04.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bada karin tallafi wa Somalia

Jamus zata bada karin tallafin kudi kimanin euro million 1 da dubu 500,wa kungiyoyin tallafawa rayuwar jamaa dake aiki a Somalia.Maaikatar harkokin waje na jamus dake birnin Berlin ta nunar dacewa hakan ya biyo bayan halin da alummomin birnin Mogadishu suka fada ne, sakamakon sabbin rigingimu da suka barke a baya.Kungiyar bada agajin kasa da kasa ta Red Cross zata karbi euro million 1,ayayinda sauran euro dubu 500 zai shiga hannun hukumar agajin bala'u daga indallahi ta jamus .Daga farkon wannan shekara kawo yanzu dai Jamus ta bada agajin euro million 4 wa alummomin somalia,da karin euro dubu 750 ,domin tallafawa yan gudun hijira na kasar dake kasahen Kenya da Habash dake makwabtaka.