Jamus na son China ta kare hakkin dan Adam | Labarai | DW | 13.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na son China ta kare hakkin dan Adam

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada bukatar da ke akwai ta aiki da doka da mutunta hakkin dan Adam a kasar China don kyautata danganta tsakanin kasashen.

Merkel ta ce yana da kyau a ce kamfanonin kasar da ma kuma shirye-shirye da za su yi na hadin gwiwa su kasance an gina su kan yanayin da yake kunshe da bin doka da oda. Shugabar ta gwamnatin Jamus na wadannan kalamai ne a wani taro da bangarorin biyu ke yi a birnin Beijing na kasar China, inda ta kara da cewar bin doka da kare hakkin bani Adama na da muhimmancin gaske.

Wannan zantawa na zuwa ne daidai lokacin da masu kare hakkin bani Adama a China ke kokawa kan yadda ake cin zarafin mutane musamman ma lauyoyi inda wata kididdiga ta nuna cewar a bazarar shekarar da ta gabata kadai an kame lauyoyi da 'yan fafutuka kimanin 300.