Jamiyar ANPP ta lashi takobin yaki da cin hanci a Najeriya | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamiyar ANPP ta lashi takobin yaki da cin hanci a Najeriya

Jamiyar ANPP a taraiyar Najeriya ta lashi takobin kakkabe miyagun halaye da cin hanci da rashawa a kasar dake yammacin Afrika.

Jamiyar ta fadi haka ne a lokacinda take sanarda wanda ta zaba a matsayin dan takarar shugaban kasar.

A dai jiya ne jamiyar ta ANPP ta tsaida tsohon shugaban mulkin soji Janar Muhammadu buhari mai ritaya,bayanda sauran yan takara 6 suka janye daf da fara jefa kuriar,suna masu fadin cewa tsohon shugaban na soji shike da kwarewa tare da dama mafi yawa na lashe zaben da zaa gudanar a 2007.