Hukuncin Babbar Kotun Zartaswa Ta Jamus | Siyasa | DW | 25.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukuncin Babbar Kotun Zartaswa Ta Jamus

A hukuncin da ta yanke a jiya alhamis babbar kotun zartaswa ta Jamus ta amince da dokar haramta dan-kwali da gwamnatin jihar Baden-Württemberg ta kafa a makarantunta.

Har yau ana ci gaba da sabani akan dan kwali a makarantun Jamus

Har yau ana ci gaba da sabani akan dan kwali a makarantun Jamus

Bisa ga ra’ayin kotun zartaswar ta Jamus, dokar haramta dan-kwali da jihar Baden-Württemberg ta kafa ba ta da nasaba da addini. Kuma duk da cewar dokar tana batu a game da kasancewar addinin Kirista daya daga cikin shika-shikan al'adun kasashen yammaci, amma ba ta fifita wani addini akan wani. Kotun ta ce dokar tayi daidai da ka’idojin da kotun koli ta zayyana kuma wata cikakkiyar kafa ce ta haramta dan kwali ga malaman makaranta a bakin aikinsu. Da wannan hukunci babbar kotun zartaswar ta Jamus ta share hanya ga jihohin kasar dake da sha‘awar gabatar irin wannan doka ta haramta dan kwali ko kuma wata almar dake bayani game da alkibla ta siyasa ko addini ko akida a makarantunsu. A takaice gwamnatin jiha na da cikakken ikon kakaba wab malaman makaranta takunkumin biyayya ga manufar nan ta ba-ruwa-na a ajujuwan koyarwa, kamar yadda yake kunshe a daftarin tsarin mulkin Jamus. Wannan hkunci, kamar yadda babbar kotun zartaswar ta nunar, Fereshta Ludin, ba ta cancanci kama aikin koyarwa a makarantun gwamnati ba, saboda kin biyayya ga wannan kuduri na dokar tsarin mulkin kasa duk kuwa da shahadarta ta kwarewa a aikin koyarwa. To sai dai kuma wannan hukuncin baya ma'’nar kawo karshen gardandamin da ake famar yi akan wannan batu saboda ba dukkan jihohin Jamus ne ke da niyyar yin koyi da dokar ta jihar Baden-Württemberg ba.

A hukuncin da ta yanke shekarar da ta wuce kotun koli mai kula da daftarin tsarin mulkin Jamus ta ce kowace jiha na da ikon haramta dan-kwalin bisa sharadin cewar zata gabatar da dokar da ta tanadi haramcin. Ita kuma jihar Baden-Württemberg ba ta yi wata-wata ba wajen zama jiha ta farko da ta gabatar da irin wannan doka a cikin watan afrilun da ya gabata. Dokar dai ba kawai ta shafi dan kwali ba ne kazalika har da duk wata shigar dake nuni da addinun mutum kamar dai irin rawanin nan na mabiya addinin Sikh a cewar Ferdinand Kirchhof masanin al’amuran shari’a a jami’ar Tübingen, wanda ya wakilci jihar ta Baden-Württemberg a kotun. Amma fa a daya hannun yayi nuni da cewar shigar nan irin ta mata masu zaman zuhudu, ba shiga ce dake nuna akidarsu ta addini ba, shiga ce ta aiki.