Gyara a sashen sufuri ta sama a Najeriya | Siyasa | DW | 05.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gyara a sashen sufuri ta sama a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sallami shugabanin hukumomi hudu da ke karkashin ma'aikatar sufurin jiragen saman kasar biyo bayan zarge-zarge cin hanci da rashin kula da aiki.

Fyaden 'ya'yan kadanyar da aka yi wa shugabanin hukumomin guda hudu da ke karkashin ma'aikatar kula da sufurin jiragen saman Najeriya, wanda ya biyo bayan zargin cin hanci da rashawa wanda ake ganin da shugabanin ne aka rinka hada baki ana aikata ba daidai ba a zamanin tsohuwar minister Stella Oduah ya jawo mai da martani mabanbanta.

Ma'aikatun da abin ya shafa da ake yi wa kalon su ne ruhin samun nasara ko akasin haka a batun harkar sufurin jiragen saman Najeriyar musamman hukumar hukumar kula da zirga-zirga jiragen saman Najeriya da aka dorawa alhakin sa ido a kan ingancin jiragen da ke sauka da tashi da na hukumar kula da filayen jiragen saman kasar, wannan ya sanya tambayar Captain Mohammed Bala Jibril kallon yunkurin a matsayin fargar jaji.

DW_Nigeria_Integration2

Goodluck Jonathan ya ce sallamar jami'an da ya yi mataki ne na daidaita al'amura

Ya ce ''Wannan ihu ne bayan hari. An riga an yi almundahana ta fitar hankali a wannan sashi domin akwai son kai da son zuciya wanda ya dade. Su wadanda aka baiwa wannan aiki na da aiki mai nauyi a kansu, kuma dama an ce in kai ya rube to sai jiki ya lalalce, saboda haka su ne yanzu in suka gyara za'a samu gyara in kuma su ka ci gaba da yadda ake to ba za'a samu canji ba. Amma gaskiyar magana ita ce har yanzu akwai sauran rina a kaba sai dai kuma baza'a ce lalacewar ta kai yadda ba za'a iya gyara ba amma zai dauki lokaci domin nan da shekaru goma ba za'a samu abinda ake bukata ba''.

To sai dai ganin an kama hanyar gyara a yanzu musamman bayan sallamar wadanan jami'ai tun daga kan tsohuwar minister da batun sayen motoci masu sulke guda biyu a kan Naira milyan 255 ya zama alura da ta tono garma a kan matsalolin da suka adabi sashin, duk kuwa da bilyoyin kudadden da gwamnati ke ikirarin kashewa. Da ya ke tsoaci kan wannan batu, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen saman Najeriya Sanata Babayo Gamawa da su na neman a yi gyara a sashin ya ce a yanzu akwai muhimmin abinda suka sanya a gaba.

Nigeria Flughafen Lagos Archivbild 2007

Rashin filayen jirage masu ingaci sun taimaka wajen tabarbarewa sufurin jiragen sama a Najeriya

Ya ce ''Abinda mu ke son mu maida hankali a kansa shi ne wajen tabbatar da kwararrun ma'aikata da kuma horaswa na wajen aiki yadda ya ke za'a tabbatar da cewa a kowane lokaci a kan kowacce naura da ke kula da sufurin jiragen sama a Najeriya akwai kwrarrun mutanen da suka san yadda za su sarrfa su, da kuma tsarin da cibiyar da ke kula da harkokin jiragen sama ta duniya da ke kasar Canada ta shimfida. Wannan shi ne abinda muka kuduri niyya muka sa a gaba kuma muna fatan Allah zai mana jagora mu samu wannan''.

Kama hanyar yin cikakken garambawul ga sashin sufurin jiragen saman Najeriya da kwarraru suka dade da bayyana damuwarsu kan mumunan cin hanci da rashawa da ya ke fuskanta da sannu a hankali ya kama hanyar ruguza sashin na zama abin da za a zura idannu a ga tasirinsa duba da irin matsayin da Najeriya ke da shi tsakanin takwaorinta na Afrika.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Muohamadou Awal Balarabe/Ahmed Salisu

Sauti da bidiyo akan labarin