EU ta yi kiran da a rusa kungiyar M23
November 1, 2013Talla
Mai magana da yawun ofishin harkokin wajen na kungiyar ta EU Sebastien Brabant ne ya yi wannan kiran, inda ya ce ya kyautu a gaggauta kammala tattaunawar da ake ta kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ke gudana a kasar Uganda, da ma dai kawo karshen kungiyar ta M23.
Baya ga wannan, Mr. Brabant ya ce akwai bukatar da ke akwai wajen ganin an dakile aiyyukan dukannin wata haramtaciyyar kungiya a kasar da ke dauke da makamai.
To sai dai a hannu guda Brabant din ya ce gwamnatin kasar ta guji daukar duk wani mataki na ramuwar gayya ko kuma cin zarafin fararen hula.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu