Bunkasa ciniki: Layin dogo tsakanin Najeriya da Nijar | Siyasa | DW | 12.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bunkasa ciniki: Layin dogo tsakanin Najeriya da Nijar

A kokari na sake bunkasar ciniki a cikin yankin yammacin Afirka, gwamnatin Najeriya da kamfanin Mota Angil sun amince da aikin layin dogon da ya hade Kano a sashen arewacin kasar da Maradi a kudancin Nijar.

Ko bayan tsohuwar yarjejeniya ta gamayya a tsakani na kasashen yankin yammmacin Afirka, daukacin kasashen nahiyar Afirka sun kaddamar da ciniki na bai daya a shekarar bana.

Abin kuma da makwabta na kasashen tarrayar Najeriya da na Nijar ke neman amfana a cikin wani sabon layin dogo da zai hade Kano da ke sashen arewacin kasar da kuma Maradi a sashen na kudancin Nijar.

Dalar Amurka miliyan dubu kusan biyu ne dai Abujar ke shirin ta batar a cikin aikin  mai tsawon kilomita 283 da kuma zai dauki shekaru dai-dai har guda uku kafin a kammala.

A shekarun baya ma dai Nijar ta kaddamar da aikin layin dogo tsakanin Yamai da Cotonou

A shekarun baya ma dai Nijar ta kaddamar da aikin layin dogo tsakanin Yamai da Cotonou

Layin dogon da ke zaman irinsa na farko na zamani da zai hade wasu kasashe a daukacin yankin na yammacin Afirka dai zai hade jihohin na Kano da Jigawa da Katsina kafin tsayawa a garin na Maradi da ke zaman iyaka a tsakanin kasashen guda biyu. 

Karin bayani: Shimfida layin dogo daga Cotonou zuwa Yamai

Kuma ko bayan batun habaka ciniki mai girma dai, kuma a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na Abujar akwai tsohon tarihi a tsakanin kasashen guda biyu da ke kokari na farfado da tsohuwar al'ada mai nisa a cikin yankin Sahel.

Karin bayani: Najeriya: Gwamnati na kokarin fadada harkar sufurin jiragen kasa

Kokarin sauyawa daga rakumi zuwa jirgi na kasa dai, ana kallon layin dogon a matsayin babbar dama ta sake inganta rayuwa cikin yankin mai miliyoyin al'umma da kuma sannu a hankali yake kallon rushewar lamura.

Shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari

Sabon layin dogon da kamfanin Mota-Angil na kasar Portugal zai gina dai na shirin yin matukar tasiri wajen jigilar kayan gona da dabbobin kiwo daga ita kanta Maradi ya zuwa jihohin na arewacin tarrayar Najeriya guda uku da birnin Legas da ke zaman babbar tashar ruwan kasar.

Abin kuma da a cewar Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa da ke zaman daya a cikin jihohin da ke shirin amfana, ke iya babban tasiri ga makoma da rayuwar al'umma.

Najeriyar dai na zaman kasa ta hudu a tsarin ciniki da makwabciyarta ta Nijar, ko bayan kasashen Faransa da Jamus da Amurka.

Kuma layin dogon na iya kaiwa ga farfadowa da kila habaka cinikin da al'umma ta kasashen guda biyu ke da bukata.

Sauti da bidiyo akan labarin