1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da shimfida layin dogo a Najeriya

March 7, 2017

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shimfida layin dogo daga Lagos zuwa Kano, kafin nan gaba a kara fadada zirga-zirga jiragen kasar zuwa wasu sauran sassa na kasar.

https://p.dw.com/p/2Yn6r
Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Hoto: DW/U. Musa

A yayin kaddamar da shimfida layin dogon mukaddashin shugaban Najeriyar Farfesa Yemi osinbajo ya tabbatar da cewar idan har akwai wasu muradai da 'yan Najeriya ke bukata babu kamar inganta harkokin sufiri,wanda kuma da wannan dama shugaban kasar ya cika alkawarin da yauka.A can baya dai Najeriya ta yi zaman tana da jiragen kasa da ke yin zirga-zirga a cikin kasar amma kuma shekaru gomai a suka wucce halin da kasar ta samun nta na tattalin arziki hakan ya janyo babban koma baya a game da lamarin na bunkasa harkkin sufirinShugaban hukumar jiragen kasa na Najeriya Usman Abubakar a lokacin da yake yin jawabi ya ce gwamnatin ta cimma manufofin da ta sa ma gaba da wannan sabon layin dogo.Kuma masu yin sharhi a kan al'ammura na hasashen cewar samar da jirgin kasar zai taimaka sossai ga bunkasa sha'annin kasuwanci a kasar.

Eisenbahn Nigeria
Hoto: DW/M.Bello