Kano ke zama birni mafi girma mai hadadar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya.
Asalin mazauna birnin Hausawa ne amma akwai sauran kabilun Najeriya da kuma baki daga kasashen ketare da suke rayuwa cikinsa. Jihar Kano ta kasance daya daga cikin jihohin Najeriya 36, kuma ta fi kowace jiha yawan kananan hukumomi inda take da 44.