Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Maradi yana cikin birane masu muhimmanci musamman kan kasuwanci da al'adu a Jamhuriyar Nijar.
Kamar sauran biranen da suke yankin Sahel akwai zafi sosai a birnin wanda ko yaushe yake cike da harkokin kasuwanci.
A Jamhuriyar Nijar hukumomin jihar Maradi na ci gaba da shirya tarurukan mahawara da zummar kawo karshen ta'addancin.
Ana ci gaba da shirya tarukan mahawara da zummar samo hanyoyin kawo karshen ta'addanci da masu garkuwa da mutane da satar dabbobi a Jamhuriyar Nijar musamman mazauna kan iyakar Katsina, Zamfara da Sokoto da ke Najeriya.
Mamakon ruwan saman da ake tafkawa a jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 190 yayin da ibtila'in ya haifar da babbar asara ga wasu da yawansu ya haura dubu dari uku.
Za a j yadda gwamnatin Anambara ta Najeriya ke kokawa kan yadda matsalolin zaizayar kasa ke cinye filaye a jihar. An soma tantance gonaki da filaye a yankunan da aikin gina hanyar jirgin kasa zai shafa a Maradin Jamhuriyar Nijar. Corona kuwa tana karuwa a Ghana, amma an ce da matakai a kasa.
Shagulgulan bikin budin daji, guda daga cikin al'adun gargajiya da masarautar Tsibirin Gobir da ke Jamhuriyar Nijar. Babban abin da yafi daukar hankalin jama'a shi ne arwa ko bugun kasa domin binciko abubuwan da za su faru cikin shekara, misali damuna da zaman lafiya ko rikici da makamantansu.
Rahotanni daga jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar na cewa akalla mutane shida sun sake mutuwa bayan ruftawar kasa a wata mahakar zinare a garin Kwandago da ke karamar hukumar Dan Issa a ranar Litinin.
A wannan karon shirin ya ziyarci matasa a Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Tarayyar Najeriya, domin tattaunawa da su kan sana'o'in da suke yi domin su dogara da kansu.
A Jamhuriyar Nijar, kayataciyyar kokowar gargajiya karo na 42 ta gudana a Yamai inda Issaka Issaka na jihar Dosso ya zama sabon sarki, bayan da ya samu nasara a kan Aibo Hassan na jihar Maradi.
Wata matashiya da ta kammala digiri a fannin fasali da ci-gaban karkara, ta yanke hukuncin kama sana'ar sayar da abinci da kai wa wurin tarururka domin dogaro da kai.
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar, sun kudiri aniyar daukar matakai domin kare rayukan yara kanana da ke makarantun reno wato Nursery. Wannan na zuwa ne bayan gobara ta lakume rayukan daliban firamare a jihar Maradi.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki aniyar rufe mahakar zinare ta garin Kwandago da ke karamar hukumar Dan Issa, sakamakon asarar rayuka da aka samu a mahakar.
A jamhuriyar Nijar an gudanar da jana’izar yara 'yan makaranta da da suka rasu a iftila'in gobara a birnin Maradi
Ku saurari shirinmu da ke zaburar da matasan Afirka doamin su tashi su nemi abin dogaro da kanus, ta hanyar zakulo wasau da tuni suka yi nisa a neman na kan nasu mu tattauna da su.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana barkewar annobar cutar amai da gudawa ko Cholera a wasu jihohi uku na kasar.