Bukukuwan Sallar Layya a kasashen duniya | Zamantakewa | DW | 23.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukukuwan Sallar Layya a kasashen duniya

A ranakun Talata da Laraba ne al'ummar Musulmi na duniya suka gudanar da shagulgulan Sallar Layya, da ke gudana kwana guda bayan hawan Arfat a kasar Saudiyya, yayin da Jamhuriyar Nijar ta yi tata sallar a ranar Laraba.

Duk da yanayin kuncin rayuwa da babbar sallar ta bana ta samu al'ummar Musulmi a ciki, an gudanar da shagulgulan sallar cikin annashuwa da yarda da kaddarar Ubangiji. Kamar yadda aka saba, an dauki tsauraran matakan tsaro a sassa daban-daban, inda a birnin Kano na Najeriya ma aka tsaurara matakan tsaron saboda hawa da masarautar Kano kan shirya a kowace shekara, inda bikin yake kara armashi.

DW.COM