Nijar: Kokarin rage barnar itacen girki | Labarai | DW | 16.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Kokarin rage barnar itacen girki

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da aniyarsu ta sa idanu domin ganin an takaita amfani da itace a lokacin bukin babbar Sallah ko kuma sallar layya.

Albarkacin babbar sallar dai birnin yamai kadai a rana daya, ana kona kusan kashi daya cikin biyar na itacen da ake iya amfani da su tsawon shekara guda. Kimanin raguna 395.000 ne dai ake yankawa a  Yamai babban birnin kasar ta Nijar a lokacin sallar ta layya, wanda wajen gashin su ake amfani da itace ton 48.000 a cewar Kanal Oumarou Alou Darektan ma'aikatar kula da muhalli ta jihar Yamai.

Mako daya kafin babbar sallar, tuni ma'aikatar kula da yanayin ta birnin Yamai ta dauki matakai na bincike domin tare duk wasu lodin itace da ake shigowa da su birnin cikin motoci ko bisa jakai, da ma cikin amalanke ba bisa ka'ida ba. Al'ummar birnin Yamai da yawanta ya kai miliyan daya da rabi, na amfani da itace ton dubu 273 a kowace shekara, abun da ake ganin ya yi yawa a kasar da ke fama da gurgusowar Hamada.