Afganistan: Tsagaita wuta don bikin sallah | Siyasa | DW | 20.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afganistan: Tsagaita wuta don bikin sallah

Al'ummar Afganistan na fatan ganin fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan Taliban, 'yan kasar dai na fatan yarjejeniyar za ta ba su damar gudanar da shagulgulan Sallar Layya.

Mayakan Taliban dai na zama karfen kafa na haifar da shakku game da zubar da jini a yawancin manyan bukuwan da ake yi a kasar. Wannan ya sa 'yan kasar da dama ke cike da fatan ganin gwamnati ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Taliban a yayin gudanar da babbar Sallah. Haji Azizullah, mazauni ne a birnin Kabul ga kuma abin da yake cewa: "Kowa da kowa na son ganin an kawo karshen yaki a Afganistan, kowa na fatan samun dauwamammen zaman lafiya a fadin kasar. Muna son dorewar zaman lafiya dan samun rayuwa mai inganci."

A yayin bikin cikar Afganistan shekaru 99 da samun 'yancin kai, Shugaba Ashraf Ghani ya sanar da bukatar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarunsa da kungiyar Taliban albarkacin hutun babbar Sallah: "Daga ranar Litinin, ranar hawan Arafat a kasa mai tsarki har zuwa ranar tunawa da haihuwar ma'aikin Allah (S.A.W), mun sanar da tsagaita bude wuta, da yarjejeniyar Taliban su ma za su ajiye makamansu har tsawon wadannan ranaku. Sanar da tsagaita wutan na nufin daga dukkanin bangarori ne, kuma tsawaita shi ya danganta da yadda kungiyar Taliban suka mutunta yarjejniyar."

Kawo yanzu dai kungiyar Taliban ba su yi martani kan tayin gwamnatin Afganistan ba, abin da ke kara fargaba a zukatan mutane a yayin da za a shiga shagulgulan babbar sallah. Haria Mosadiq mai bincike ne a kungiyar Amnesty kan yakin na Afganistan, yana ganin idan dukkanin bangarorin za su kauce wa cin zarafin al'umma, za a samu bakin zaren warware matsalar da kasar ke ciki. A baya dai gwamnatin Afganistan ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan Taliban a karamar sallah, sai dai a wannan karo yayin da 'yan kasar ke dakon cimma irin wannan yarjejeniya an wayi gari da labarin kungiyar Taliban ta yi garkuwa da akalla mutane 150, sai dai bayanai na cewa sojojin gwamnati sun kubutar da su.

Sauti da bidiyo akan labarin