Ana ci gaba da shagulgulan sallah a Najeriya | Siyasa | DW | 21.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ci gaba da shagulgulan sallah a Najeriya

Dukkan masallatai da ke Kano sun cika makil da al'ummar Musulmi manya da yara, inda aka gudanar da sallar Idi tun da sanyin safiya.

A hudubar da ya gabatar a masallacin Jakara daya daga cikin masallatan Kano da aka yi sallar Idi, Malam Karibulla Sheikh Ibrahim Abubakar Ramadan ya kiri daukacin Musulmi da su kasance masu tsoron Allah su kuma kiyaye da umurninsa da kuma haninsa.

Daga bisani Limamin ya yi matashiya dangane da nau'i na dabbobi da za su yi layya da su, da shekarunsu da kuma lafiyarsu.

Duk da yanayin kuncin rayuwa da babbar sallar ta bana ta zo wa al'ummar Musulmi, ana ci gaba da gudanar da shagulgulan salla cikin annashuwa da yarda da kaddarar Ubangiji.

Kamar yadda aka saba, an dauki tsauraran matakan tsaro saboda hawa da masarautar Kano kan shirya a kowace shekara, kuma abin sai kara armashi yake yi.

Sauti da bidiyo akan labarin