Berlin za ta ci gaba da hulda da Moscow | Labarai | DW | 29.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Berlin za ta ci gaba da hulda da Moscow

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce akwai dalilai masu yawa da zasu sanya su ci gaba da yin huldar makamashi da kasar Rasha.

Angela Merkel ta bayyana hakan ne a Berlin baban birnin kasar, yayin wani taron manema labarai da suka gudanar tare da Firaministan kasar Finland Alexander Stubb, inda ta ce duk da takunkumin da suka kakaba wa Rasha sakamakon irin rawar da ta ke takawa a rikicin Ukraine, a yanzu haka za su ci gaba da huldar makamashi da ita zuwa wani lokaci. Ta kara da cewa komai yana iya sauyawa, in har Moscow ta ci gaba da taka mummunar rawa a rikicin Ukraine. Merkel ta ce yana da kyau a ci gaba da yin matsin lamba ga Rasha, kuma a halin yanzu bata ga wani dalili da zai sanya a saukakawa Moscow takunkumin da suka kakaba mata ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu