Birnin Moscow shi ne inda fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin take. Kimanin mutane miliyan 12 ne ke zaune a birnin.
Moscow shi ne birni mafi girma a Rasha kuma shi ne ya fi kowanne birni girma a nahiyar Turai. Birnin na cike da kayan tarihi wanda suka hada da fadar Kremlin da kuma majami'ar St. Basil.