1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Umerov ya zama ministan tsaron Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
September 4, 2023

Reznikov ya mika takardar murabus, kwana guda bayan da Shugaba Zelensky ya sanar da maye gurbinsa da wani jami'i na daban sakamakon badakalar cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/4VwcY
Ministan tsaron Ukraine mai murabus Oleksij ResnikoHoto: Heiko Becker/REUTERS

A tsukin fiye da shekara guda da rabi da Ukraine ta shafe tana yaki da Rasha, ministan tsaro Oleksiï Reznikov ya kasance daya daga cikin jami'an siyasa da na soja da suka samu karfin fada a ji, inda yake balaguro a kai-a kai zuwa kasashen waje domin neman agajin kayan yaki a hannun kawayen Kiev na yammacin duniya.

Amma kwatsam shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa zai maye gurbinsa da Rustem Umerov mai shekaru 41, wani fitaccen shugaban al'ummar Tatar na yankin Crimea, wanda ya wakilci Kiev a baya a wata tattaunawa da Moscow kafin a nada shi a matsayin mai kula da harkokin sayar da kadarorin gwamnati.

Duk da cewa tsohon Minista Reznikov ya mika takardar murabus ga majalisar dokoki, amma har yanzu bangaren bai kada kuri'a don tabbatar da wannan sauyi a ma'aikatar ta tsaro ba. Sai dai wannan mataki ya zo ne a yanayi na farmakin da take kai wa sojojin Rasha, yayin da Zelensky ya yi alkawarin karfafa yaki da cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare a Ukraine.

Ukraine | Unabhängigkeitstag in Kiew | Wolodymyr Selenskyj
Hoto: kyodo/dpa/picture alliance

Dama dai Kungiyar Tarayyar Turai ta gindaya wa Kyiv sharadin kawar da cin hanci idan tana son a mutunta matsayinta na takarar zama memba. Dmytro Duginov, lawya da ke zama a birnin Kyiv ya ce wannan murabus ya yi daidai, duba da girman matsalar cin hanci da rashawa:

"Ina ganin cewar murabus ne da ya zo a kan kari; an samu rahotanni da dama a kafafen yada labarai na cewa ma’aikatarsa ​​na da hannu a cikin almundahana a fannin sayo kayayyaki. Ban ji wani bayani mai ma'ana daga gare shi lokacin da yake magana a talabijin ko kuma ta yanar gizo ba."

A baya-bayan nan dai, badakalar cin hanci da rashawa da dama ne aka bankado a kasar ta Ukraine, inda daya daga cikinsu ya shafi Oleksiï Reznikov kai tsaye dangane da kwangilar kayan aikin soja da aka sanya hannu tare da wani kamfanin na kasar Turkiyya.  Sai dai a daidai lokacin da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai hari a wasu wurare na Ukraine, Shugaba Zelensky ya yi alkawarin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.

Oleksiï Reznikov dai, an nada shi ministan tsaron Ukraine watanni uku kafin mamayar da Rasha ta yi wa kasar a ranar 24 ga Fabrairu, 2022.  Sai dai mazauna Kyiv na sukar aikinsa bayan da y mika takardar murabus, kamar yadda wani soja mai shekaru 53 mai suna Ihor ya bayyana.

"Na yi imanin cewa dole ne a tuhume shi kan abin da ya aikata a lokacin da ya rike mukamin ministan tsaro musmaman ma kan badakalar farashin kayan abincin sojoji da ma na kayan sawan sojoji.Dole ne a tuhume shi da akalla a kan wannan laifi."

Tun bayan dakatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuli da ya bai wa Ukraine damar fitar da hatsinta ta tekun Bahar Asuwad, Rasha ta kara kai hare-haren bama-bamai a wannan yanki na kasar Ukraine wanda ya kunshi tashoshin jiragen ruwa da sauran masana'antu masu muhimmanci ga wannan ciniki. Sai dai sojojin Ukraine sun yi ikirarin harbo jirage marasa matuka 22 daga cikin 25, yayin da sojojin Rasha suja ce sun kai wani samame a tashar jiragen ruwa da ke yankin Odessa.

Ukraine | Präsident Selenskyj Frontregion nahe Saporischschja
Volodymyr Zelensky da manyan jami'an sojin kasarsaHoto: President Of Ukraine/APA Images/Zumapress/picture alliance

Amma masanin ilimin halin dan Adam mai suna Vladyslav ya yaba da turjiya da ya nuna lokacin yaki da sojojin Rasha

"Da alama dai komai na tafiya salin alin. Na ji dadin halayyar da ya nuna da abin da ya yi a baya. Tabbas akwai badakalar cin hanci, kuma watakila murabus da ya yi yana da alaka da su. Amma babu wata shaida. Tun da a san sunan sabon ministan tsaro, wannan yana da kyau."

Sai dai sauya ministan tsaron Ukraine bai hana shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi domin tattauna batun farfado da  yarjejeniya  fitar da hatsi Ukwaine ta  Bahar Asuwad ba. Erdogan da ke zama daya daga cikin shugabannin kungiyar tsaro ta NATO da ke da alaka mai kyau da Putin, yana fatan yin amfani da wannan dama wajen yin shawarwarin zaman lafiya tsakanin Kiev da Moscow, yayin da Ukraine ta samu kanta a cikin jerin hare-hare.