Kiev shi ne babban birnin kasar Ukraine. An samo asalin sunan birnin daga sunan mutumin da ya kafa shi wato Kyi.
Birnin na da mutanen da suka tasamma miliyan uku kuma baya ga kasancewarsa babban brinin kasar Ukraine, Kiev na daga cikin biranen kasar da suka yi fice a duniya.