1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta shirya tura makamai Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
August 23, 2022

Jamus ta shirya tura makamai da kudinsu ya kai Euro miliyan 500 zuwa Ukraine, domin taimaka wa kasar a yakinta da Rasha, a cewar kakakin shugaban gwamnati Olaf Scholz.

https://p.dw.com/p/4FwJW
ILA - Internationale Luft- und Raumfahrtausstellung in Berlin
Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

Kiev na shirin karbar makamai da suka hadar da na kare kanta da motocin yaki masu sulke da wasu muhimman kayan fada a cewar sanarwar da aka gabatar a wannan Talata, a dai dai lokacin da kansilan ke ziyara a Canada.

Ba da jimawa ba ne dai Scholz ya yi alkawarin karin gagarumin taimakon kudi da tallafin soji wa Ukraine. Tun a farkon wannan shekarar ce dai Jamus din ta yi ta kokonto kan ko ya dace ta taimakawa Ukraine da makamai, batun da ya haifar da jinkiri mai tsawo da kuma kace-ka na ce a cikin gida da waje.