1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta kai farmaki kan jirgin yakin Rasha

June 9, 2024

Ukraine ta yi ikirarin lalata jirgin yakin Rasha mafi girma da shahara wanda ke ajiye a rumbun adana makaman Moscow, bayan gwamnatin Kyiv ta samu tallafin kayan yaki daga yammacin duniya don kare kanta.

https://p.dw.com/p/4gq4b
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyj a yayin da yake gaisawa da takwaransa na Amurka Joe Biden
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyj a yayin da yake gaisawa da takwaransa na Amurka Joe Biden Hoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Ma'aikatar tsaron Ukraine ta fitar da hotunan jirgin yakin da ta lalata samfurin Su-57, wanda Shugaba Vladimir Putin ke makutar alfahari da shi. Wasu hotunan kuma sun nuna yadda wani bangare na jirgin ya lalace.

Karin bayani: NATO: Tattauna karin makamai ga Ukraine

Harin na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurka da Jamus suka bukaci Ukraine da ta kutsa har cikin Rasha domin maida martani, ta hanyar amfani da sabbin makaman yakin da suka bawa Keiv tallafi.

Karin bayani: Ukraine ta yi shelar dakile harin Rasha da jirage marasa matuka

Ya zuwa yanzu dai fadar Kremlin ba ta yi martani kan ikirarin Ukraine din ba tukuna, sai dai Rashar ta sanar da kakkabo wasu jiragen yakin Ukraine mara matuka guda uku a lardin Astrakhan.