1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta dakile harin Ukraine a Donetsk

Abdullahi Tanko Bala
June 5, 2023

Ma'aikatar tsaron Rasha a birnin Moscow ta ce sojojinta sun dakile wani gagarumin hari na Ukraine a gabashin yankin Donetsk

https://p.dw.com/p/4SBwS
Russland | Schäden durch Militärangriff auf Donezk
Hoto: Valentin Sprinchak/dpa/TASS/picture alliance

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron  Rasha Igor Konashenkov ya ce abokan gabar sun yin yunkurin karya lagon tsaro a yankunan al'umma masu rauni amma basu yi nasara ba.

Babu tabbas ko harin da Ukraine ta kai na daga cikin matakin daukar fansa da ta shirya wanda aka dade ana jira domin sake kwato yankunan da Rasha ta mamaye.

A waje guda kuma wasu jirage guda biyu marasa matuka sun fada kan wata babbar hanya a yankin Kalunga a kasar Rasha sai dai ba a sami fashewar wani abu ba. Hukumomi sun ce an killace wurin da lamarin ya faru.

Rasha ta ce sojojinta sun kashe sojojin Ukraine 250 tare da lalata tankokin yaki da dama.