1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong Un zai tattauna da Putin

Abdourahamane Hassane
September 11, 2023

Jagoran Koriya ta Arewa Kim Jung Um na kan hanyarsa ta zuwa Rasha domin ganawa da Shugaba Vladmir Putin.

https://p.dw.com/p/4WDQI
Russland Nordkorea Gipfel in Wladiwostok | Kim Jong Un und Putin
Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP Photo/picture alliance

Kamfanin dilancinlabaran Koriya ta arewan KCNA ya ce shugaba Kim Jong Un ya shiga jirgin kasa mai sulke wanda harsashe ba ya hudawa domin isa a birnin Moscow inda zai tattauna batun cinikin makamai da Rasha za ta saya daga Koriyan saboda halin da take cikinsa na yaki da ukraine. Masu aiko da rahotanin na cewar Kim Jong ya fi son yin doguwar tafiya  da jirgin kasa, a maimakon na sama kamar mahaifnsa saboda jikara da yake da ita, kan cewarAmirka na iya kai masa hari.