1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Diflomasiyya ta yi tsami tsakanin Jamus da Rasha

May 31, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta aike wa fadar Moscow da takardar rufe wasu kananan ofisoshin jakadancin Rasha da ke kasarta.

https://p.dw.com/p/4S1SK
Estland | Bundeskanzler Scholz in Tallinn
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus ta yanke shawarar rufe hudu daga cikin kananan ofisoshin jakadancin Rasha biyar da ke kasarta, a matsayin ramuwar gayya kan mataki diflomasiyya makamancin wannan da Moscow ta dauka a kanta.

A lokacin da yake bayani a birnin Berlin a kan wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya shaidawa taron manema labarai cewar, wannan mataki ne na rama wa kura aniyarta.

Baya ga haka a watan Nowamba mai zuwa Jamus din za ta rufe kananan ofisoshin jakadancinta da ke kasar Rasha da suka hadar da na biranen Kaliningrad da Ekaterinbourg da kuma Novossibirsk.