1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fidda tsarin aike abinci Afrika

July 21, 2023

Rasha ta ce tana sane da damuwar kasashen Afrika kan matakinta na ficewa daga yerjejeniyar fitar da hatsi ta teku daga Ukraine, tare da yin alkawarin samar da mafita ga kasashe mabukata wadanda da take dasawa da su.

https://p.dw.com/p/4UFD2
Hoto: ALEXEY BABUSHKIN/SPUTNIK/AFP

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Verchinine ne ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai da ya yi, inda ya ce Moscow ba za ta bar kasashe abokan huldarta na nahiyar Afrika cikin matsalar abinci ba. Sergueï Verchinine ya kuma kara da cewa tun tuni Moscow ta fidda tsari na aike abinci i zuwa daukacin kasashen da za su halarci taron Rasha da kasashen nahiyar Afrika, wanda za a gudanar a birnin Saint-Petersbourg a karshen wannan wata na Yuli.

Duk da kokarin shawo kanta da MDD da kuma Turkiyya ke yi don amincewa da dorewar yerjejeniyar fitar da abinci ta teku daga Ukraine, har kawo yanzu Rasha ta dage kan cewar sai an ba ta dama kamar Ukraine domin fitar da kayan abincinta da kuma sinadaren hada takin zamani. Sai dai kasashen Yamma da suka makara wa Rashar takunkumai sun ki amincewa da wannan sharadi.