Turkiyya kasa ce wacce bangarenta na yamma wanda ya fi girma ke cikin yankin yammacin Asiya yayin da daya sashen ke yankin kudu maso yammacin Turai.
Kasar na da iyaka da Iran da Iraki da Armeniya da Azarbaijan da Jojiya da Bulgeriya da Girka. Kasancewarta tsakanin Turai da Asiya ya bata muhimmanci a fannin diflomasiyya da cinikayya.