Bataliyar farko ta sojin kiyaye zaman lafiyar Eu ta isa Kongo | Labarai | DW | 08.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bataliyar farko ta sojin kiyaye zaman lafiyar Eu ta isa Kongo

Zangon farko na bataliyar sojin kiyaye zaman lafiya karkashin kungiyyar hadin kann turai sun fara isa kasar Kongo.

Bataliyar sojin dai an shirya cewa zasu taimakawa jami´an tsaron kasar ne wajen tabbatar da doka da kuma oda ,a lokacin zaben shugaban kasar.

An dai shirya yin wannan zabe ne mai dimbin tarihi, kuma irin sa na farko a tsawon shekaru 40 a kasar ne a ranar 30 ga watan juli na wannan shekara.

Masu fashin baki na siyasa dai na ganin cewa, matukar ba a gaggauta daukar matakan tsaro akan lokaci ba, zaben ka iya fuskantar koma baya a sabili da hali na rashin cikakken tsaro.