Isa Yuguda tsohon gwamnan Jihar Bauchi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kana tsohon ministan sufurin jiragen sama.
Isa Yuguda an haife shi a shekarar 1956 kuma ya yi aikin bankuna da dama da shugabancin wasu bankuna biyu zuwa shekara ta 2000, daga bisani ya zama karamin minista a gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo.