Annan ya yi tir da tarzomar da ta halaka ´yan gudun hijirar Sudan a Masar | Labarai | DW | 31.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi tir da tarzomar da ta halaka ´yan gudun hijirar Sudan a Masar

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi Allah Wadai da matakan karfi da ´yan sandan Masar suka dauka akan ´yan gudun hijirar Sudan. Mista Annan ya ce mutuwar akalla mutane 20 a lokacin kwashe ´yan gudun hijirar da karfin tuwo daga wani sansanin wucin gadi, wani bala´i ne da babu wata hujjar da zata kare shi. Rahotannin dai sun ce fiye da mutane 20 suka rasu lokacin da jami´an tsaron Masar suka yi amfani da karfi wajen ta da ´yan gudun hijirar Sudan daga wannan sansani dake birnin Alkahira. A wani labarin kuma shugaba Hosni Mubarak ya nada sabbin membobin majalisar ministocinsa, inda ba´a samu wani canji ba a manyan mukamai. FM Ahmed Nasif da ministan harkokin cikin gida Habib al-Adli zasu ci-gaba da rike mukamansu. ´Yan adawa da kungiyoyin kare hakkin ´yan Adam sun zargi ministan da hannu a tashe tashen hankulan da suka wakana a lokutan zaben ´yan majalisar dokoki.